in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin makamashin hasken rana
2016-07-22 10:27:25 cri

Kasar Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin makamashin hasken rana (AAE), kusan dalar Amurka biliyan 1,75, tare da wasu kamfanoni goma sha hudu, ta yadda kasar za ta cimma karfin wutar lantarki zuwa Megawatts (MW) 1125.

Yarjejeniyoyin suna burin nuna niyyar gwamnatin Najeriya yawaita bangaren wutar lantarki na kasar, in ji ministan makamashi, ayyuka da gidajen kwana, mista Babatunde Fashola, wanda ya rattaba hannu da sunan gwamnatin Najeriya.

AAE sun kasance tushe da ruhi na zuba jari a bangaren wutar lantarki, in ji ministan, tare da jaddada cewa, nan da shekarar 2030, kashi 30 cikin 100 na karfin Najeriya zai kasance wajen samar da wutar lantarki daga makamashi mai tsabta.

Mista Fashola ya bayyana cewa, zamani inda kasar take dogaro da hanya guda ta samar da makamashi ya wuce.

Ya kuma kara da cewa, Najeriya ta zabi kafa irin wadannan gine ginen samar da makamashin hasken rana a yankunan arewaci da ake samun hasken rana sosai fiye da sauran yankunan kasar. Ministan ya bayyana jin dadinsa kan yadda masu zuba jari suka nuna yarda sosai a cikin wadannan ayyuka domin zuba yari a bangaren makamashin Najeriya.

Ya tabbatarwa masu zuba jari cewa, gwamnati za ta yi kokarin shimfida wani yanayi mai kyau ga zuba jari, amma tare da yin kashedi cewa, ba zai rufe ido ba kan aiwatar da wadannan ayyuka ba bisa inganci ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China