in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 8 suka mutu a tsakiyar Afrika tun farkon shekarun 1990 sakamakon yake yake kabilanci
2016-10-01 12:33:01 cri
Kusan mutane miliyan takwas suka mutu a tsakiyar Afrika tun farkon shekarun 1990 ya zuwa wannan lokaci dalilin yake yake kabilanci da na addini, in ji Mohamed Rukara mai shiga tsakani na kasar Burundi a ranar Jumma'a a birnin Bujumbura.

Wannan adadi yana nuni sosai domin tunatar da kowa wajen kawar da wannan ciwo dake janyo illa ga miliyoyin mutane, koda a takaita shi a yankin tsakiyar Afrika, in ji mista Rukara a yayin wani bikin rufe wani dandalin kasa da kasa kan matsayin masu shiga tsakani da shugabannin addinai kan rigakafin yake yaken kabilanci da na addini, da aka gudanar a bujumbura daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Satumba.

Tsakanin addinai da dama da kuma tsakanin hukumomin shiga tsakani, yayi kira cewa dole a bunkasa wani tsarin hadin gwiwa bisa tsawon lokaci na tuntubar juna da tattaunawa domin kawar da tunanin rarrabuwar kawuna da na tashin hankali.

Mahalarta wannan dandali sun fito daga nahiyar Afrika, Asiya da kuma Turai, kuma sun fito daga addinai daban daban.

Mista Rukara ya bayyana cewa yayi farin ciki na ganin cewa mahalartan dandalin sun goyi bayan gabatar da shawarwari ga gwamnatoci dasu sanya su a cikin tsare tsaren bada horo game da horar da 'yan kasa, ta yadda mutane zasu san da farko su 'yan kasa ne kafin su san su mamba ne na wata kabila.

Haka kuma ya nuna yabo kan yadda wannan dandali ya gayyaci gwamnatoci wajen karfafa kasa mai 'yanci da kuma girmama 'yancin kananan kabilu da addinai, domin kawar da sake barkewar koda yaushe yake yaken siyasa, kabilanci da na addinai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China