in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sham ta yi suka kan harin da kawancen da ke yaki da IS ya kai mata
2016-09-19 08:31:16 cri

Kafofin yada labarai na kasar Sham sun ba da labari a jiya Asabar cewa, kawancen sojojin kasa da kasa da ke yaki da kungiyar IS karkashin jagorancin Amurka ta kai hari ta sama kan sansanin sojojin kasar Sham a wannan rana, lamarin da ya halaka sojoji fiye da 10.

Kamfanin dillancin labarai na Sham ya ruwaito sanarwar da sojojin kasar Sham suka bayar dake cewa, kawancen sojojin kasa da kasa ya kai hari kan sansanin sojojin kasar dake tsauni al-Tharda dake dab da filin saukar jiragen sama na Deir Ez-Zor dake gabashin kasar ta Sham, lamarin da ya lalata na'urori da mutane da dama. Sanarwar ta ce, matakin sojin ya keta 'yancin kasar Sham da sojojinta.

A nata bangarea, hukumar tsaron kasar Amurka ta fitar da wata sanarwa a wannan rana cewa,sai da sojojin kawancen suka gudanar da bincike kafin su kai hari kan sansanin a wannan yanki,kuma suna ganin cewa, wannan sansanin kungiyar IS ne mai tsatsauran ra'ayi.

Sanarwar ta ce, sojojin kawance sun taba kai hari kan wannan wuri a baya, kuma ta nanata cewa, ana fuskantar yanayi mai sarkakiya a kasar Sham, haka kuma a kullum sojojin gwamnati musayar wuta da masu fafutuka, a saboda haka, zai wahala su kai hari kan sojojin gwamnatin kasar Sham da gangan. Hukumar ta ce, lokacin da sojojin kawancen suka fahimci cewa wannan sansanin sojojin gwamnatin Sham ne, nan da nan suka dakatar da harin.

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil-adama ta Sham mai hedkwata a birnin London ta ce, hari ta sama da aka kai a wannan karo ya yi sanadin mutuwar sojojin gwamnatin Sham 83, kana sojojin fiye da 120 suka ji rauni. Hukumar tsaron kasar Rasha ta ba da wata sanarwa cewa, harin ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar Sham 62. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China