in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali: wani sojan Faransa ya mutu sakamakon taka nakiyar da aka binne a karkashin kasa
2016-11-06 12:38:54 cri

Ranar 5 ga wata, fadar shugaban kasar Faransa ta ba da wata sanarwa, inda a cewarta, wani sojan Faransa ya rasa ransa sakamakon taka wata nakiyar da aka binne a karkashin kasa yayin da yake gudanar da aikinsa cikin wata mota mai sulke a arewacin kasar Mali wadda ke yammacin nahiyar Afirka a ranar 4 ga wata da yamma.

A cikin sanarwar, fadar shugaban Faransa ta nuna girmama wa ga wannan sojan kasar tare da jajantawa iyalinsa. A cikin sanarwar, François Hollande, shugaban Faransa ya nuna imaninsa ga sojojin Faransa da ke gudanar da aiki a Mali, tare da karfafa kwarin gwiwarsu sosai.

Bisa labarin da kafofin yada labaru na Faransa suka bayar, an ce, bayan da gwamnatin Faransa ta tura sojojinta zuwa Mali domin taimaka kasar wajen tabbatar da kwanciyar hankali tun a shekarar 2013 har zuwa yanzu, sojojin Faransa 18 suk rasa rayukansu a Mali.

Tun bayan da sojojin Mali suka yi juyin mulki a shekarar 2012, wasu kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda sun mamaye arewacin kasar sakamakon rashin kwanciyar hankali. A watan Janairu na shekarar 2013, bisa ga bukatun gwamnatin Mali, gwamnatin Faransa ta tura sojojinta zuwa Mali domin taimakawa takwarorinsu na Mali maido da zaman lafiya. A watan Afrilu na shekarar 2013, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin kafa rundunar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Mali.

A watan Mayu na shekarar 2015, gwamnatin Mali da wasu dakarun da ke rike da arewacin kasar sun sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da samun sulhu, kana a ranar 20 ga watan Yuni, sassa daban daban masu ruwa da tsaki na kasar sun daddale yarjejeniyar a matakin karshe. Amma duk da haka, tun bayan shekarun da suka wuce, har yanzu ana cigaba da samun rikici a arewacin Mali. Har ila yau a tsakiyar Mali kuma, tashe-tashen hankali da hare-haren ta'addanci suna karuwa a 'yan kwanakin baya bayan nan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China