in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mali: MDD ta yi kiran dukkan bangarori da su tabbatar da zabukan kananan hukumomi ba tare da matsala ba
2016-11-20 12:22:51 cri

A ranar Asabar, Sakatare Janar na MDD, Ban Ki-moon ya amince da matakin da gwamnatin kasar Mali ta dauka na shirya zabukan kananan hukumomi a ranar Lahadi 20 ga watan Disamban shekarar 2016.

Mista Ban ya amince cewa, kundin tsarin mulkin Mali na watsi da wani sabon matakin dage zabe, wanda tuni aka taba dage wa har sau uku.

Sakatare Janar na yarda cewa, muhimman jinkirin da aka samu wajen aiwatar da muhimman matakan yarjejeniyar zaman lafiya da kuma sasantawa a Mali, game da kafa hukumomin wucin gadi, da kuma matsalar tsaro a arewacin kasar da wasu yankunan dake tsakiyar kasar, za su iya kawo tarnakaki ga shirya zaben, in ji kakakin Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa.

Haka kuma, mista Ban ya tabo shakkun da wasu jam'iyyun siyasa da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya suka gabatar game da gudanar da zabukn kananan hukumomi kan ranar da aka tsaida. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China