in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fursunoni 93 sun tsere a kasar Mali
2016-12-07 11:23:29 cri

Jiya Talata, ma'aikatar tsaron kasar Mali ta ce, a wannan rana da sassafe, wasu dakarun da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan wani gidan kurkuku da ke birnin Niono da ke tsakiyar kasar, inda masu gadi 2 suka jikkata, yayin da wasu fursunoni 93 suka tsere.

Wani gidan telibijin mai zaman kansa a Mali ya labarta cewa, a wannan rana da karfe 2 na safe, wasu dakaru sun kai hari a gidan kurkukun, tare da 'yantar da dukkan fursunoni. Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta yi shelar daukar alhakin kai harin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China