in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: manufar Sin daya tak ba abin da za a iya shawarwari a kai ba ne
2017-01-15 12:48:08 cri
A ranar Asabar, Mista Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya kalubalanci wasu bangarorin kasar Amurka da su fahimci muhimmancin batun Taiwan, da tsayawa kan alkawarin da shugabannin kasar Amurka suka yi a baya, don kula da maganar Taiwan yadda ya kamata.

Kakakin ya yi furucin ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ciki har da tambayar da aka yi cewa, a kwanakin baya zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ambaci huldar dake tsakanin Amurka da Sin, inda ya ce dukkan al'amura, ciki har da manufar kasar Sin daya tak, za a iya shawarwari a kai, dangane da batu, ko mene ne ra'ayin kasar Sin?

Mista Lu Kang ya amsa cewa, a duniyarmu akwai kasar Sin daya tak, sa'an nan Taiwan ta kasance wani bangare na harabar kasar, wadda ba za a iya balle ta ba. Ya kara da cewa, gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar Sin ita ce halaltacciyar gwamnati guda daya tak da za ta iya wakiltar kasar Sin, wannan shi ne hakikanin ra'ayi da gamayyar kasa da kasa suka amince da shi, kuma ba wanda zai iya canza shi.

Manufar kasar Sin daya tak a duniya ita ce tushen huldar dake tsakanin Sin da Amurka, ba wani abu da za a iya shawarwari a kai ba ne, in ji kakakin kasar Sin. Ya ce, Sin ta kalubalanci wasu bangarorin kasar Amurka da su fahimci muhimmancin batun Taiwan, da aiwatar da alkawuran da gwamnatin kasar Amurka ta dauka a baya, wato bin manufar kasar Sin daya tak, da bin ka'idojin da aka tanada cikin manyan sanarwoyi 3 wadanda bangarorin Sin da Amurka suka sanar tare, da kula da batun Taiwan yadda ya kamata, ta yadda za a magance illa ga huldar dake tsakanin kasashen 2 da hadin gwiwarsu a wasu fannoni masu muhimmanci.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China