in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NPFL: Wasanni sun kankama kuma tuni Rangers ta kwashi rashin nasara
2017-01-18 15:48:41 cri
Yayin da ake ci gaba da fafatawa a wasannin farko farko a gasar Firimiyar Najeriya na kakar bana wato na shekarar 2016/2017, kungiyar MFM FC ta Lagos ta fara buga wasa da kafar dama, inda ta doke Niger Tornadoes da ci 3 da nema, a wasan da suka buga a filin wasa na Agegen jihar Lagos.

Dukkanin bangarorin biyu dai sun bude wuta tun take wasan, amma dan wasa Sikiru Olatunbosun ne ya fara jefa kwallo a ragar Niger Tornadoes, kafin kuma daga bisani Stephen Odeh, da Adekunle Adegboyega su kara nasu kwallayen, aka kuma bar Niger Tornadoes na mamakin yadda aka haihu a ragaya.

A wasan birnin Enugu kuwa, Enugu Rangers ta sha mamaki a hannun Abia Warriors, inda kungiyar ta Abia ta doke Enugu Rangers din a gida da ci 2 da 1.

Ita kuwa kungiyar Enyimba wadda ta rike kambin gasar a baya, ta fara wasan ta ne da samun nasara, bayan da ta doke Sunshine Stars da ci daya mai ban haushi, a wasan da suka buga a Calabar. Ibrahim Mustapha Musa na Enyimba ne ya ciwa kungiyar ta sa kwallon ta raba gardama, minti guda kafin tafiya hutun rabin lokaci.

A filin wasa na Muhammad Dikko dake jihar Katsina kuwa, Katsina United da Gombe United ne suka fafata, aka kuma tashi masu masauki wato Katsina United na da kwallo 2 Gombe na da 1.

Wasan Wikki Tourists da Nasarawa United kuwa tashi aka yi ba ci. Yayin da ita kuwa Plateau United ta bi Remo Stars har gida ta jefa mata kwallaye 2 da 1, a wasan da ya gudana a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China