in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjinawa shawarar dawo da Keshi bakin aikin sa
2014-11-05 16:30:00 cri
Hukumar gudanarwar kwallon kafar Najeriya NFF ta amince da rokon babban daraktan kwamitin kwararrun ta Shaaibu Amodu, game da mai da kocin kulaf din kasar Stephene Keshi bakin aikin sa.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya samu kwafin ta ta ce hukumar ta NFF ta samu takardar shawara da Shaaibu Amodu ya aike mata a ranar 27 ga watan Oktoba, yana mai rokon hukumar ta maida Keshi kan aikin horas da Super Eagles.

A ranar 16 ga watan Oktobar da ya shude ne dai hukumar ta bayyana sunan Shaibu a matsayin wanda zai maye gurbin Keshi, jin kadan bayan da Sudan ta doke Najeriya 3 da 1, a birnin Abuja, a ci gaba da buga wasannin share fagen gasar kwallon kafar nahiyar Afirka dake tafe. Sai dai Shaaibu ya ce daukar wannan mataki bai dace ba. Ya ce ba shi da damar shirya 'yan wasa da sauran tsare-tsare da za su bashi damar tinkarar wasanni biyu da suka ragewa kulaf din na Super Eagles.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China