in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakamakon gasar Firimiyar Najeriya
2016-09-07 19:18:10 cri
A ci gaba da buga gasar kwallon kafar firimiya ta Najeriya mako na 34, Enugu Rangers ta doke Rivers United da ci 4 da nema, wanda hakan ya bata damar darewa saman teburin gasar, yayin da kuma Kano Pillars ita ma ta jefawa Sunshine Stars ta garin Akure kwallo 2 ba ko daya. Sai kuma kungiyar Lobi wadda ta zurawa mai rike da kambin gasar wato Enyimba kwallo da 1 mai ban haushi, a wasan da suka buga a ranar Lahadin karshen mako.

Yanzu dai Enugu Rangers ce ta daya a teburin gasar da maki 54 cikin wasanni 32 da ta buga, sai kuma Rivers United wadda ta sauko zuwa matsayi na biyu da maki 53. Wikki Tourists, wadda a baya ke saman teburin ta dawo matsayi na uku da maki 51. Sai kuma Lobi stars a matsayi na 4 da maki 49.

Duk da nasarar da Kano pillar ta samu a gida kan Sunshine Stars ta Akure, Pillars din na da jimillar maki 48, kuma ta 9 a teburin gasar. Sauran wasannin da aka buga sun hada da Akwa United wadda ta lallasa MFM FC da ci 3 da 1, sai Plateau United wadda ta doke Shooting Stars ta Ibadan da ci daya mai ban haushi, yayin da kuma Warri Wolves ta samu nasara kan Nasarawa United da ci daya da nema.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China