in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gasar ITF/CAT: Adetunji, da McLeod zasu jagoranci tawagar Najeriya
2016-02-05 16:34:37 cri
Hukumar kwallon Tennis ta Najeriya, ta fidda sunayen 'yan wasan ta da zasu wakilci kasar, a gasar 'yan wasa matasa ta ITF/CAT ta bana, wadda za ta gudana a birnin Tunis, na kasar Tunisia, tsakanin ranekun 7 zuwa 13 nan na Fabarairu.

Babban kocin tawagar matasan 'yan kasan 'yan shekaru kasa da 18 Mohammed Ubale, ya ce 'yar wasan kasar wadda ke rike da kambin gasar ajin 'yan kasa da shekaru 16 Adetayo Adetunji, da kuma Angel McLeod ne za su jagoranci tawagar kasar.

Ubale ya ce 'yan wasan biyu, sun taimakawa Najeriya wajen ci gaba da rike kambin ta na gasar West & Central AJC da aka gudanar a birnin Abuja cikin watan Janairun da ya gabata, a kuma wannan karo za su kare kasar, tare da sauran 'yan wasa irin su Andiyo Inwang. Inwang wadda haifaffiyar kasar Jamus ne, za ta wakilci Najeriya kamar yadda haifaffiyar kasar Rasha Melissa Ifidzhen ta wakilci Najeriyar a bara.

Ifidzhen dai ta taka rawar gani ga Najeriya, inda a bara ta buga wasa ga kasar. Kafin hakan, ita 'yar wasar Najeriya dake zaune a Landan Elizabeth Garos-Pam, da Ifidzhen sun buga wasa su biyu, inda suka kai matsayin wasan kusa da na karshe a shekarar 2014.

A baya bayan nan 'yan wasan Najeriya mafiya taka rawar gani a wasan Tennis, sun hada da Candy Idoko, wadda ta kai ga wasan karshe na 'yan wasa biyu, da kuma wasan kusa da kusan na karshe a gasar 'yan wasa daya-daya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China