in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar wasannin Najeriya ta bukaci 'yan wasan Super Eagles da su ja damarar dauko kofin zakarun Afirka
2016-01-14 14:30:03 cri
Ministan wasannin da matasa na tarayyar Najeriya Solomon Dalung, ya ja hankalin 'yan wasan kungiyar kwallon kafar kasar Super Eagles dake wasa a gida, da su dage wajen ganin sun dauko kofin zakarun Afirka a gasar da kasar Rwanda za ta karbi bakuncin ta nan da 'yan kwanaki.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN, ya rawaito minista Dalung, na cewa yana fatan kungiyar 'yan wasan kasar za ta dora daga inda aka tsaya, game da nasarorin da kungiyar 'yan kwallon kasar ke samu a baya bayan nan.

Shi ma a nasa tsokaci, shugaban hukumar kwallon kafar kasar NFF Mr. Amaju Pinnick, kira yayi ga 'yan wasan gida na kungiyar ta Super Eagles, da kada su baiwa Najeriya kunya, yana mai cewa akwai bukatar su daga matsayin kasar a wannan gasa, wadda hukumar kwallon kafar Afirka wato CHAN ke shiryawa.

A gasar karshe ta CHAN wadda aka buga a Afirka ta Kudu, Najeriya ce ta zamo ta 3, bayan da Libiya ta dauki kofin, kana kasar Ghana ta kasance ta 2. Gasar ta bana ita ce za ta zamo karo ta 4, tun fara gudanar da ita a shekarar 2009.

A wani ci gaban kuma, 'yan wasan gida na Super Eagles sun doke kasar Cote d'Ivoire da ci 1 mai ban haushi, a wasan sada zumunci da suka buga a ranar Litinin, gabanin bude gasar ta CHAN. Wasan da ya gudana a filin wasa na Tuks dake birnin Pretorian Afirka ta kudu.

Sakamakon sauran wasannin da kungiyar wadda koci Sunday Oliseh ke horaswa sun nuna cewa Super Eagles din ta buga kunnen doki 1-1 da kasar Angola a makon da ya gabata, kafin nan kungiyar Amatuks ta Afirka ta kudu ta doke Super Eagles din da 3 da nema.

Ana dai sa ran Super Eagles din za ta isa birnin Kigali a ranar 15 ga watan nan na Janairu, inda za ta taka leda da kasashen Nijar, da Tunisia, da kuma Guinea a rukunin C, a zagayen gasar na farko, wadda za ta gudana tsakanin ranekun 16 ga watan Janairu ya zuwa 7 ga watan Fabarairu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China