160225-barcelona-zai-kafa-kwalejin-wasan-kwallon-kafa-a-najeriya-bello.m4a
|
Ambode ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin manyan jami'an kulob din, wanda ya zama na gaba-gaba a duniya ta fuskar fasahar wasan kwallon kafa.
Gwamnan ya bayyana wannan al'amari a matsayin wani babban abin tarihi a jihar, sannan ya bayyana cewar abin farin ciki ne, kasancewar lamarin ya zo dai dai lokacin da gwamnatin ke shiye shiryen karbar bakuncin wasannin gudun famfalaki wato marathon na kasa da kasa.
Ambode ya bayyana muhimmancin wasanni wajen samar da ci gaba, ya kara da cewer, harkar wasanni tana taimakawa musamman wajen samar da ayyukan yi ga matasan jahar ta Legas.
Pau Vilanovai Vila-Abadal, shi ne daraktan harkokin kasuwanci, na kungiyar wasannin kwallon kafa ta Barcelona, ya kuma bayyana cewa Barcelona ta yanke shawarar kafa kwalejin ne a Legas, saboda yawan al'umma da jihar ke da shi, da kuma samar da damammaki ga jihar.(Ahmad Fagam)