in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta goyi bayan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen yakar ta'addanci bisa doka
2016-10-10 20:05:09 cri
A yayin wani taron manema labaru da aka saba shiryawa a yau Litinin a nan Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya yi bayani kan "dokar gudanar da adalci ga masu nuna goyon bayan ta'addanci" wadda aka zartas da ita a majalisun dokokin kasar Amurka, inda Mr. Geng ya jaddada cewa, bangaren Sin yana goyon bayan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen yakar ta'addanci bisa dokokin kasa da kasa, da ka'idodin tabbatar da dangantakar hulda tsakanin kasa da kasa, kuma bai kamata dokokin cikin gida ta wata kasa su wuce matsayin dokokin kasa da kasa ba.

A kwanan baya ne dai aka zartas da "dokar gudanar da adalci ga masu nuna goyon bayan ta'addanci" a majalisun dokokin kasar Amurka, inda aka yarda kowane Ba'amurka ya kai karar gwamnatin kasar waje a gaban kotun kasar Amurka, bisa wasu matsalolin ta'addanci da suka faru a kasar Amurka, kuma suka haifar da mutuwar Amurkawa. Sakamakon haka, wasu kasashe sun mai da hankulansu sosai kan wannan doka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China