Sunday Thomas, shi ne darakta janar na kamfanin Inshora na Najeriya (NIA), ya yi wannan kira ne a Legas, birnin kasuwancin kasar, inda ya bukaci gwamnatoci su tabbatar da girke jami'an tsaro a makarantun kasar.
Thomas, ya kuma yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a wani masallacin dake jami'ar Maiduguri a jahar Borno, dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, wanda wani yaro dan shekaru 7 ya kaddamar da harin kunar bakin wake, lamarin da ya haddasa mutuwar wani farfesa da wasu mutane 4. (Ahmad Fagam)