in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya damu matuka game da karuwar rikicin kabilanci a Sudan ta Kudu
2016-11-19 17:12:47 cri
A daren jiya Juma'a, kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwa ta kafofin watsa labaru, inda ya nuna damuwa matuka game da karuwar rikicin da ake samu a tsakanin kabilu daban daban na kasar Sudan ta kudu a yan kwanakin nan, kwamitin ya kuma yi Allah wadai da duk wani farmaki da ake kaddamarwa a kan fararen hula, da kuma yada maganganun dake kara ruruta wutar tashe tashen hankula a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, mambobin kwamitin suna ganin cewa rikicin siyasa da ya kaure a kasar Sudan da kudun ya dauki sabon salo, inda ya rikide zuwa fadan kabilanci wanda ake cigaba da fuskanta a halin yanzu. Sakamakon haka, kwamitin sulhun ya yi kira ga gwamnatin kasar ta sudan ta kudu da ta dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, don rage yin amfani da nuna karfin tuwo, da kuma inganta warware rikici a tsakanin al'umma. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China