Minista Onyeama wanda ya bayyana hakan a Abujar, fadar mulkin Najeriya, ya ce shugaba Jammeh zai martaba muradun al'ummarsa da kiraye-kirayen da kungiyoyi da sauran kasashen duniya ke yi masa na ganin an warware takaddar siyasar kasar, duk da matsayin da ya dauka na kin amincewa da sakamakon zaben wanda tun farko ya amsa shan kaye.
Ya ce, Najeriya a nata bangaren za ta ba da gudummawar da ta dace na ganin an kawo karshen matsalar siyasar cikin ruwan sanyi.
Shugaba Jammey dai ya sha kaye a hannun Adama Barrow ne a zaben shugabancin kasar da ya aka gudanar . (Ibrahim)