in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci bangarori daban daban a Gambia da su kai zuciya nesa
2016-12-11 13:40:10 cri
Jiya Asabar, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa ta kafofin watsa labarai, inda ya yi kira ga bangarori daban daban a kasar Gambia da su kai zuciya nesa, su guji yin tashin hankali a wannan kasa.

Sanarwar ta kuma nuna cewa, mambobin kwamitin sulhu na MDD sun yi maraba da kuma yabawa al'ummomin kasar Gambia dangane da gudanar da babban zaben kasar da aka yi cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da boye kome ba a ran 1 ga wata. Shi ya sa, mambobin kwamitin sulhu na MDD ta zargi sabuwar sanarwar da shugaban kasar Yahya Jammeh ya gabatar a ran 9 ga wata, inda ya bayyana cewa, ya ki amince da sakamakon babban zaben da aka yi, ya kuma bukaci a sake yin sabon zaben shugaban kasar.

Dangane da wannan lamari, kwamitin sulhu na MDD ya fidda sanarwar cewa, ya kamata Yahya Jammeh ya mutunta zaben da al'ummomin kasar suka yi, sa'an nan, ya mika ragamar mulkin kasar ga dan takakar da ya lashe babban zaben shugaban kasa, wato Adama Barrow. Haka kuma, mambobin kwamitin sulhu na MDD sun sa kaimi ga Yahya Jammeh da ya tabbatar da mika ragamar mulkin kasar cikin yanayin zaman lafiya.

Haka zalika, mambobin kwamitin sulhu na MDD za su ci gaba da sa ido kan canje-canjen yanayin siyasa a kasar ta Gambia.

A daren ranar 9 ga wata, shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh wanda ya kasa fadi a babban zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 1 ga watan, ya yi wani jawabi ta gidan talabijin, inda ya sanar da cewa, bai amince da sakamakon babban zaben shugaban kasa ba, kuma ya bukaci a sake gudanar da babban zaben shugaban kasar ta Gambia.

Daga bisani kuma, Yahya Jammeh ya yi gargadi cewa, kada al'ummomin kasar su ki amincewa da kudurin da ya yi, kana kar su yi zanga-zanga a kasar dangane da wannan batu.

A ranar 2 ga watan nan da muke ciki ne, kwamiti mai kula da harkokin zabe na kasar Gambia ya sanar da cewa, Adama Barrow ne ya lashe babban zaben shugaban kasar da aka yi a ran 1 ga wata, inda ya samu kuri'u kashi 45.5 bisa dari, kuma hakan ya tabbatar da cewa Mr. Barrow ne zai dare kan kujerar shugaban kasa a watan Janairu na shekarar 2017 mai zuwa.

Babban zaben shugaban kasa da aka yi a kasar Gambia na wannan karo, ya kasance karo na biyar da aka gudanar da a Gambia bayan Yahya Jammeh ya hau kan kujerar shugaban kasar a shekarar 1994 sakamakon wani juyin mulki da ya yi. Haka kuma, Mr. Jammeh ya lashe babban zaben kasar da aka yi a shekarar 1996, sa'an nan, ya ci gaba da lashe babban zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar 2001, shekarar 2006 da kuma shekarar 2011. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China