in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na kan bakanta kan manufar kasar Sin daya tak a duniya
2017-01-13 09:11:39 cri
Babban mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya game da harkokin watsa labarai Garba Shehu, ya ce tuni Najeriya ta amince da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma da ma wannan ce manufar kasar a tsawon lokaci.

Garba Shehu ya ce kuskure ne a rika yada cewa Najeriya ta yanke alaka da yankin Taiwan, domin kuwa da ma can alakar dake tsakanin sassan biyu ta kasuwanci ce, ba cikakkiyar huldar diflomasiyya ba, wanda kuma hakan ba zai sauya ba.

A wani ci gaban kuma, shugaban kwamiti mai kula da basussukan waje da na cikin gida a majalissar dattawan Najeriya sanata Shehu Sani, ya jinjinawa manufar kasar game da wannan batu, yana mai cewa hakan zai kawo karshen wasu dabaru da ake amfani da su, a yunkurin nema wa Taiwan gindin zama a Najeriyar a wasu fannoni da ka iya sabawa doka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China