in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta baiwa baki 'yan kasashen waje 335 shedar zama 'yan kasa
2017-01-12 09:48:29 cri

A jiya Laraba gwamnatin Najeriya ta amince da baiwa baki 'yan kasashe waje 335 da suka nemi izinin zama a kasar yayin da ta yi watsi da bukatun wasu 165 na neman gindin zama a kasar.

Minsitan cikin gida na Najeriyar Abudulrahman Dambazau, ya shedawa 'yan jaridu bayan kammala taron majalisar zartaswar kasar a Abuja fadar mulkin kasar.

Dambazau ya ce kwamitin ministoci dake kula da bada shedar zama dan kasa, sama da mutane 500 ne suka mika bukatun neman izinin zama a kasar. Kuma daga cikinsu gwamnatin kasar ta amince da baiwa mutane 335 wadanda suka cika ka'idar samun izinin zama a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China