in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta rufe ofishin jakadancin Taiwan dake Abuja
2017-01-12 09:31:14 cri

Mahukunta a Najeriya sun bayyana rufe ofishin jakadancin yankin Taiwan dake birnin Abuja fadar mulkin kasar, tare da umartar wasu daga ma'aikatan sa da su koma birnin Legas, domin gudanar da huldodin da suka shafi cinikayya bisa doka.

Ministan harkokin wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, jim kadan bayan kammala taron manema labarai na hadin gwiwa, tare da takwaransa na kasar Sin Wang Yi.

Mr. Onyeama ya kara da cewa, Taiwan za ta daina cin gajiyar matsayi na kasa mai cin gashin kan ta a Najeriya, duba da cewa ba ta da wannan hurumi a matsayi na kasa da kasa, da ma manufar da Najeriyar ke bi tsakanin ta da sauran kasashen duniya.

Daga nan sai ministan ya kara nanata matsayin Najeriyar game da amincewa da wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China