Yayin ganawar ta su, shugabannin 2 sun yaba wa kyakkyawar hulda tsakanin kasashen 2, kuma sun yarda da tsayawa kan manufar bude kofa, gami da hakuri da bambancin ra'ayi, don kara zurfafa huldar hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2.
Shugaban Xi na kasar Sin ya ce, yadda kasashen Sin da Switzerland suka kulla sabuwar huldar abokai da ta shafi manyan tsare-tsare, yana da ma'anar gaske. Don haka kamata ya yi, shugabannin bangarorin 2 su kara musayar ra'ayi, da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa.
Mr. Xi ya ce kasar Sin na fatan daukar muhimman matakai tare da Switzerland, a fannin hadin gwiwar kirkiro sabbin fasahohi. Kaza lika Sin na son ci gaba da cudanya tare da Switzerland, musamman ma a fannonin fasahar kwamfuta, da masana'antun zamani, da dai sauransu.
A nata bangaren, shugabar kasar Switzerland ta ce, ci gaban da kasar Sin ta samu a bangarorin tattalin arziki, da zamantakewar al'umma ya burge jama'ar kasar Switzerland sosai, musamman ma nasarorin da Sin ta samu wajen rage talauci, da kyautata zaman rayuwar jama'arta.
A sabili da haka, kasar na son ci gaba da hadin kai tare da kasar ta Sin, a fannonin da suka shafi cinikayya, da hada-hadar kudi, da kirkiro sabbin fasahohi, da al'adu, da dai makamantansu.(Bello Wang)