in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci bikin da membobin majalisar tarayyar Switzerland suka shiya masa
2017-01-16 10:29:35 cri
A jiya Lahadi ne a birnin Berne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin maraba da zuwa da membobin majalisar tarayyar Switzerland suka shirya masa.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin, shugaba Xi ya jaddada fatansa na zurfafa hadin-gwiwa tare da kasar Switzerland daga dukkanin fannoni, da kara raya huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashen biyu. Xi ya ce, zai halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya gami da ziyartar wasu kungiyoyin kasa da kasa dake kasar ta Switzerland, a wani mataki na cimma maslaha tare da bangarori daban-daban kan wasu muhimman batutuwan duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China