Xi Jinping gami da uwargidansa Peng Liyuan sun yi tattaunawa cikin armashi da annashuwa tare da Madam Leuthard gami da mai gidanta, inda Xi ya ce, yayin ziyararsa a wannan karo, yana fatan zurfafa mu'amala tare da takwararsa Madam Leuthard da sauran wasu muhimman jami'an gwamnatin Switzerland, da karfafa hadin-gwiwar kasashen biyu daga dukkanin fannoni. A cewar Xi, Sin da Switzerland na da ra'ayoyi masu kama da juna da dama a wasu batutuwan kasa da kasa, wannan ya sa Sin na fatan inganta cudanya tare da Switzerland a wasu manyan harkokin duniya.
A nata bangaren, Madam Leuthard ta bayyana cewa, kasarta na fatan karfafa hadin-gwiwa tare da kasar Sin. Ta ce, Sin kasa ce dake taka muhimmiyar rawa a fadin duniya. Yayin da duniya ke fuskantar abubuwa na rashin tabbas a halin yanzu, kasashe daban-daban na alla-allar jin ra'ayin gwamnatin kasar Sin yayin jawabin da shugaba Xi Jinping zai gabatar a wajen taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya wato dandalin Davos.(Murtala Zhang)