Rundunar sojin Najeriya mai yaki da ayyukan Boko Haram, ta ce ta tattara wasu mutane da suka kai a kalla 1,240, wadanda ake zargin wasu daga cikin su mayakan Boko Haram ne, yayin ayyukan sintiri da dakarun ta ke yi a dajin Sambisa.
Da yake tabbatar da hakan a jiya Laraba a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, jagoran rundunar 'Operation Lafiya Dole" Manjo Janar Lucky Irabor, ya ce cikin wadanda ake tsare da su, akwai maza 413, da mata 323, sai kuma yara maza 251 da kuma 'yara mata 253.
Irabor ya ce, yanzu haka ana ci gaba da yiwa wadannan mutane tambayoyi, domin tantance ko akwai fararen hula na gaskiya a cikin su. Kaza jami'in sojin ya ce, dakarun sa na ci gaba da bin sawun 'yan ta'addan da suka tsere, za kuma su fada koma nan da 'dan lokaci, duba da cewa, an riga an toshe dukkanin hanyoyin su na tserewa.
A wani ci gaban kuma, Mr. Irabor ya tabbatar da cewa, wasu 'yan Boko Haram da suka tsere su kimanin 30 sun mika kan su ga rundunar hadin gwiwa dake Nijar, wadda ke aiki a wani yanki na tafikin Chadi, tuni kuma aka garzaya da su jihar Difa a Janhuriyar ta Nijar.
Mayakan kungiyar Boko Haram dai sun hallaka mutane da yawan su ya kai 15,000, tare da raba wasu sama da miliyan 2 da matsugunnan su, cikin shekaru kusan 7 da suka shafe suna kaddamar da hare hare.
Daga baya kungiyar ta bazu daga tungar ta dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, zuwa makwaftan kasashe kamar Nijar, da Kamaru da kuma Chadi.(Saminu)