in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Najeriya sun kubutar da karin mutane 1,880
2016-12-22 20:03:37 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kara kubutar da wasu fararen hula, wadanda yawan su ya kai 1,880 daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram a yankunan arewa maso gabashin kasar.

An dai kubutar da mutanen ne bayan bata-kashin da dakarun rundunar suka yi da mayakan kungiyar a dajin Sambisa, wanda a yanzu haka shi ne tungar kungiyar.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafin ta a Alhamis din nan, ta rawaito babban kwamandan dakarun sojin Najeriyar dake jihar Borno Lucky Irabor, na cewa baya ga wadannan aka samu damar cetowa ,sojojin sun kuma cafke mayakan Boko Haram kimanin 504, ciki hadda wasu 19 da suka mika wuya da kan su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China