A jiya Lahadi, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming, ya zanta da 'yan jaridun kamfanin dillancin labaran Sin Xin Hua a birnin Paris, inda ya ce, batun Kudus, wani batu ne mai sarkakkiya a rikicin Falasdinu da Isra'ila. Don haka kasar Sin ke fatan bangarorin masu ruwa da tsaki, za su yi kokarin shimfida zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra'ila bisa adalci, kuma su kaucewa matakai da ka iya kara dagula batun.
An gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya bisa tayin kasar Faransa, taron da ya guda ranar 15 ga wata a birnin Paris, inda wakilai daga kasashe gami da kungiyoyin kasa da kasa kimanin 70 suka halarta, ciki har da kasar Sin.(Murtala Zhang)