in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaba Xi Jinping ya halarci bikin ta'aziyya na tsohon shugaban kasar Isra'ila Peres
2016-10-01 13:22:34 cri
Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma mataimakin shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin kuma ministan harkokin kimiyya da fasaha Wan Gang ya halarci bikin ta'aziyya na tsohon shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres a birnin Kudus a jiya ranar 30 ga watan Satumba. A madadin shugaban kasar Sin Xi Jinping da gwamnatin kasar da jama'arta, Wan Gang ya nuna ta'aziyya game da rasuwar Peres, da nuna jajantawa ga shugaban Isra'ila Reuven Rivlin, firaminista Benjamin Netanyahu, shugaban majalisar dokokin Yuli-Yoel Edelstein da sauran shugabannin kasar da kuma iyalan Peres.

Wan Gang ya bayyana cewa, Mr Peres masanin siyasa ne na kasar Isra'ila, wanda ya sa kaimi ga kokarin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, kuma jama'ar kasar Isra'ila har ma kasa da kasa sun nuna masa girmamawa sosai. Kafin rasuwarsa, ya yi kokarin sada zumunta a tsakanin Isra'ila da Sin, da bada gudummawa sosai kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Sin ta dora muhimmanci sosai ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shekarar mai zuwa shekara ce ta cika shekaru 25 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Isra'ila, Sin za ta yi kokari tare da kasar Isra'ila wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, da sa kaimi ga samun babban ci gaba wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Reuven Rivlin, Benjamin Netanyahu, da Yuli-Yoel Edelstein sun bukaci Wan Gang da ya isar da sakon gaisuwarsu ga shugaba Xi Jinping, firaminista Li Keqiang da shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China