Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yau Talata a yayin taron manema kabarai a nan birnin Beijing, ya ce a lokacin wannan ziyara, shugaba Xi zai kuma halarci taron shekara-shekara na dandalin tattalin arziki na duniya(WEF) karo na 47 wanda zai gudana a ranar 17 ga wannan watan, bisa gayyatar shugaban dandalin Klaus Scwab.
Haka kuma,a ranar 18 ga watan na Janairu, ana sa ran shugaba Xi zai kai ziyara ofishin MDD da ke birnin Geneva da hukumar lafiya ta duniya (WHO), da hedkwatar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics da ke Lausanne dukkansu bisa gayyatar shugabanninsu bi da bi.(Ibrahim)