in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bayar da sharhi a jaridar kasar Switzerland
2017-01-13 17:00:41 cri

A yau Jumma'a ne,shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da sharhi mai taken "zurfafa hadin gwiwa da neman samun bunkasuwa cikin lumana tare"  a jaridar NZZ ta kasar Switzerland kafin ya tashi zuwa kasar Switzerland da halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na shekarar 2017 tare da kai ziyara hukumomin kasa da kasa dake kasar Switzerland.

Ya ce, a halin yanzu, hadin kan Sin da Switzerland na iya amfanawa jama'arsu, tare da sa kaimin bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Turai, da samar da gudummawa a kokarin da ake na tabbatar da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen duniya, da farfado da tattalin arzikin duniya da kuma yin ciniki cikin 'yanci.

Xi Jinping ya bayyana cewa, ziyarar da zai kai birnin Davos ita ce karo ta farko a wannan shekara, yana fatan za a kara yin musanyar ra'ayi, da karfafa imani kan tinkarar kalubale, don farfado da tattalin arzikin duniya. Sin za ta ci gaba da samar da kasuwanni ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da zama kasar da kasashen waje suke sha'awar zuba jari, da kuma kara amfanawa jama'ar kasa da kasa gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China