Da safiyar yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasar Switzerland domin kai ziyara a bisa gayyatar da kwamitin kasar Switzerland da Doris Leuthard yake jagoranta ya yi masa. Kana Xi zai halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2017 da za a gudanar a birnin Davos bisa gayyatar da shugaban gudanarwa na dandalin tattaunawar Klaus Schwab ya yi masa. Hakazalika kuma, Xi zai kai ziyara a cibiyar MDD dake birnin Geneva, da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da kwamitin wasannin Olympics na duniya wato IOC bisa gayyatar da babban sakataren MDD Antonio Guterres da babbar direktar hukumar WHO Margaret Chan da shugaban kwamitin IOC Thomas Bach suka yi masa.
Tawagar shugaba Xi a wannan karo sun hada da matarsa Peng Liyuan, memban hukumar harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Wang Huning, sakatare na sakatariyar kwamitin tsakiya na JKS Li Zhanshu, da memban kwamitin gudanarwa na kasar Sin Yang Jiechi da dai sauransu. (Zainab)