Taron na yini biyu, ya kuma zo dai-dai da cikon shekaru 50 da kafa kungiyar ta G77 wadda ke da mambobin kasashe masu tasowa 133.
Mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin Chen Zhu ya halarci taron a matsayin manzon musamman na shugaba Xi Jinping na Sin.
Chen ya bayyana kudurin Sin na kara karfafa hadin gwiwa da kungiyar ta yadda za a bunkasa ci gaba da makomarta. (Ibrahim)