Shugabar kungiyar Nkoana-Mashabane kana ministar kula da harkokin kasa da kasa ta kasar Afirka ta kudu ta bayyana hakan ne kwana guda gabani ganawar da shugabannin kasashen duniya za su yi don cimma daidaito kan manufofin samun dauwamammen ci gaba na MDD.
Ta ce, kungiyar kasashen na G 77 da Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen tsara ajandodin da suka shafi ci gaba mai dorewa da kuma sauyin yanayi, kuma za su ci gaba da yin hakan a madadin al'ummomin da aka mayar da su saniyar ware a duniya.
Madam Nkoana-mashabane ta ce, baiwa kungiyar ta G 77 irin wannan dama zai taimaka musu matuka ganin cewa, su ne ke da kasashe da dama a sassa daban-daban na duniya.
Ta kuma yi maraba da abubuwan da ke kunshe cikin ajandar samun bunkasuwa bayan shekara 2015, wadda ake saran shugabannin kasashen duniya za su amince da ita yayin taronsu a yau Jumma'a.
Ita dai wannan ajanda tana bayani ne kan nauyin da ke kan kasashe masu sukuni da marasa karfi wajen magance matsaloli kamar matsalar canjin yanayi da rashin daidaito da ake fuskanta a duniya.(Ibrahim)