Liu Jieyi, wakilin kasar Sin na din din din a MDD ya bubakci hakan a wani bikin majalissar da aka yi a cibiyar nan a birnin New York, inda Kasar Bolivia ta mika ragamar jagorancin kungiyar G77 ga kasar Afrika ta kudu.
Mr Liu yace akwai tabbacin cewa karkashin jagorancin kasar Afrika ta kudu, kungiyar ta G77 tare da kasar Sin zasu cigaba da al'ada mai kyau na goyon bayan juna da hadin gwiwa sannan kuma zasu cigaba da ganin ana samar da cigaba a kasashe masu tasowa tare.
Wakilin yace a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, Kasar Sin tana mutunta ayyukan kungiyar ta G77 matuka da kuma hadin gwiwar ta tare da kasar Sin.
Wannan kungiyar itace mafi girma ta kasashe masu tasowa a tsakanin gwamnatocinsu, wadda ke da zummar inganta tattalin arzikin da samar da daidaito a cikin al'ummomin kasa da kasa. Fatimah