in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude taron kungiyoyin kasashe 77 da Sin don tattauna batun wanzar da ci gaba
2014-06-15 16:13:41 cri
A daren ranar Asabar 14 ga watan nan ne aka bude taron kungiyar kasashe masu tasowa 77 tare da kasar Sin, a birnin Santa Cruz dake Gabashin kasar Bolivia, taron da ake fatan zai karkata ga tattauna hanyoyin yaki da fatara, da sauyin yanayi da kuma wanzar da kudurorin ci gaba bayan shekarar 2015.

Taron na kwanaki biyu da aka yiwa lakabi da "sabon tsarin rayuwa na duniya", ya zo gabar da ake cika shekaru 50 da kafuwar wannan kungiya, wadda a yanzu ke kunshe da sama da kasashe masu tasowa 130 tare da kasar Sin karkashin inuwar MDD.

Cikin jawabinsa na bude taron, babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya yi fatan wannan kungiyar ta G77 tare da Sin, za su lalubo sabbin dabaru da tsare-tsare, wadanda za su taimaka wajen kawo karshen rabuwar kai tsakanin kasashen Arewa da na Kudancin duniya, tare da daukar matakan aiwatar da sauye-sauye, ga kudurorin ci gaba bayan shekarar 2015.

Mr. Ban ya yi imanin cewa hadin gwiwar kasashe mambobin wannan kungiya, zai bada gudummawa wajen cimma nasarar yaki da fatara, ya kuma samar da dama maras iyaka ga daukacin al'ummun dake sassan wannan duniya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China