Yayin taron aikin tattalin arziki na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an nuna cewa, a shekara mai zuwa, kasar Sin za ta ci gaba da kara zurfafa kwaskwarima kan tsarin samar da kayayyaki, kana za ta kara daukar matakai domin kyautata wannan aikin karkashin sabbin yanayin da ake ciki, tare kuma da samun ci gaba a fannoni biyar, hakan ya bayyana sabuwar manufar da kasar Sin za ta aiwatar domin gudanar da kwaskwarimar tattalin arziki a shekarar 2017.
Yayin taron, an gabatar da cewa, za a kara zurfafa kwaskwarima kan tsarin aikin gona a kasar. Masani tattalin arziki na bankin masana'antun kasar Sin Lu Zhengwei ya bayyana cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake gudanar da kwaskwarima kan tsarin aikin gona shi ne kara kyautata ingancin kayayyakin aikin gona da ake samarwa ga al'ummar kasar, tare kuma da yiwa tsarin farashin kayayyakin aikin gona, da tsarin sayen kayayyakin aikin gona kwaskwarima, kana za a zurfafa kwaskwarima kan tsarin ikon mallakar gonaki a kauyuka, wanda a karshe za a cimma burin samar da wadata ga manoman kasar ta Sin.
Lu Zhengwei ya kara da cewa, akwai bukatar kara fahimtar sabuwar ma'ana ta kwaskwarimar tattalin arziki a kasar (Jamila)