Shirin da hukumar lura da teku ta kasar Sin ta sanar da shi a jiya Alhamis, ta tanadi kokarin inganta amfani da makamashin teku da aka sabunta ta hanyar gudanar da gwaje-gwaje da kuma bunkasa fasaha da kayayyakin aiki.
Shirin ya kuma kunshi karfafa bincike da kirkire-kirkire da suka danganci batun na sabunta makamashin ruwa.
A cewar shirin, makamashin da za a sabunta daga ruwa ya hada da makamashi da ake samu daga karfin tafiyar ruwa da banbancin yanayi da kuma sinadarin Biomass. ( Fa'iza Mustapha)