in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kasance kan gaba a kasuwar sabon makamashi a duniya a bara
2017-01-09 13:51:24 cri
Wani rahoton da cibiyar nazarin tattalin arzikin da ya shafi makamashi da hada-hadar kudi ta kasar Amurka ta fitar kwanakin baya ya nuna cewa, a shekara ta 2016, yawan jarin da kasar Sin ta zuba a fannin sabon makamashi a kasashe waje ya karu da kashi 60 bisa dari, wadda darajarsa ta kai dala biliyan 32, al'amarin da ya sa Sin ta kasance a kan gaba a kasuwar sabon makamashi a fadin duniya.

Shugaban wannan cibiya Mista Tim Buckley ya ce, kasuwar makamashi mai tsabta na bunkasa sosai a duniya, kuma Amurka ce ke biye da kasar Sin a wannan fanni.

A wani labarin kuma, hukumar kula da makamashin da ake iya sabuntawa ta duniya ta yi hasashen cewa, cikin guraben ayyukan yi miliyan 8.1 a fannin sabon makamashi a duniya, kasar Sin ta samar da guraben miliyan 3.5, yayin Amurka ta samar da dubu dari 8 kawai.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China