Kwanan baya, kasar Sin ta kaddamar da shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo 13, game da bunkasa makamashin da ake iya sake amfani da shi.
Wani jami'in hukumar kula da harkokin makamashi na kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta kara zuba jarin da yawansa zai kai kudin Sin yuan biliyan 2500 a fannin makamashin da ake iya sake amfani da shi, kamar wanda ake samarwa ta ruwa, da iska, da hasken rana, da na halittu, da na zafin karkashin kasa, da teku da dai sauransu.
Sa'an nan kuma, kasar Sin za ta yi kokarin magance matsaloli da ake iya fuskanta a fannin tsare-tsare, a kokarin tinkarar matsalolin da ke biyo bayan samar da makamashin da ya haura bukata daga ruwa, da iska da hasken rana. (Tasallah Yuan)