Sanarwar dai ta hadin gwiwa ce wanda hukumar kula da makamashi da kuma hukumar gudanar da al'amurran teku ta kasar suka fitar, tace, aikin samar da makamashi ta hanyar karfin iska a teku ba zai gaza kilomita 10 ba daga mashigin cikin teku, kana zurfin ruwan ba zai wuce zai kai a kalla mita 10 ba idan har an gwada fadin ruwan ya haura kilomita 10.
Sanarwar tace shirin ba zai shafi tekunan da aka kebe su musamman domin kiyaye muhallinsu ba, da kuma wadan da ake gudanar da harkokin sufuri ta cikinsu, da wuraren tarihi, da manyan wuraren kama kifi da sauran tekuna da aka haramta amfani dasu.
Dokokin sun shafi tsara shirin cigaba da, da ayyukan da aka amince dasu, da amfani da tekuna da tsibirrai, da kuma kare muhalli da gudanar da gine gine.