An ce, za kuma ta rika sarrafa kwal bisa fasahar CTL, aikin da zai lashe kudi da yawansu ya kai Yuan biliyan 55. Kaza lika masana'antar za ta rika sarrafa kwal har ton sama da miliyan 20 zuwa narkakken mai da yawansa ya kai ton miliyan 4.05 a kowace shekara, matakin da zai kawo karshen dogaronta da kasashen waje a fasahar sarrafa kwal har ya zama mai. Hakan kuma zai sa kasar Sin ta lalubo wata sabuwar hanyar sarrafa ma'adinin kwal dake cike da fasahohin zamani.
Sin dai na da tarin ma'adanin kwal, sai dai ba ta da isasshen danyen mai da iskar gas. Don haka kasar ke fatan wannan fasaha ta narka kwal, za ta tallafa mata wajen cimma burin samar da isasshen makamashi a cikin gida, tare da rage yawan iska mai gurbata muhalli dake fitarwa a birane da garuruwa.(Saminu Alhassan, Murtala Zhang)