Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta ce, za ta bunkasa makamashi ta hanyar amfani da tsirrai domin rage kona sinadarin kwal da kuma samar da kyakkyawan yanayi na iskar da ake sheka cikin shekaru 5 masu zuwa.
Hukumar kula da makamashin ta kasar, ta ce Sin ta kuduri aniyar samar da makamashi ta hanyar tsirrai tsakanin shekarar nan ta 2016 zuwa shekara ta 2020, inda take sa ran samar da kimanin ton miliyan 58 na makamashi ta hanyar tsirrai.
Shi dai makamashi ta hanyar tsirrai, ana samar da shi ne ta hanyar shuke shuke, da kuma bishiyoyin lambu wadanda ake sarrafa su domin samar da makamashi wanda zai iya ba da dumi, bayan an sarrafa shi, sinadarin ne zai samar da makamashin daga jikin tsirrai.
Gwamnatin kasar Sin ta lashi takobin samar da makamashi ta hanyar tsirrai domin tsabtace tattalin arzikinta, wanda zai dace da yanayi. Kana gwamnatin Sin ta kuduri aniyar samar da kashi 20 cikin 100 a shekarar 2030, daga kashi 11 da take da shi a halin yanzu na makamashin maras gurbata muhalli.
A halin yanzu kwal shi ne babban sinadarin da kasar ta fi dogara a kansa wajen samar da makamashi.(Ahmad Fagam)