Ofishin hukumar tsaro da wanzar da zaman lafiya da aka fi sani da Civil Defence, dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar, ya ce an kaddamar da binciken ne bayan gano cewa, mayakan boko haram sun yi amfani da bam da ake kayyade masa lokacin tashi a hare-haren da suka kai ranar Lahadin da ta gabata a babban birnin jihar wato Maiduguri.
Hukumar Civil Defence ta ce irin na'urar kirga lokaci, na ba masu kai hari damar sanin lokacin da bam din zai tashi.
Shugaban ofishin hukumar Civil Defence na jihar Borno, Ibrahim Abdullahi ya ce tun da yanzu an gano irin na'urar da 'yan tada kayar baya ke amfani da ita, to za su bi diddigi don gano daga inda suke samu.
Nijeriya ta samu nasara kwarai a yakin da take da kungiyar Boko Haram, inda jami'an tsaron kasar da ke yankin arewa maso gabas da ayyukan na Boko Haram ya fi kamari, suka karya lagonsu, ta hanyar fattatakar daga tungarsu dake dajin sambisa. ( Fa'iza Mustapha)