in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta hana shigo da tumaturin daga kasashen waje
2017-01-11 09:26:51 cri
Gwamnatin Najeriya ta bullo da fasahar sarrafa tumatur domin rage shigo da tumaturin da aka sarrafa daga kasashen waje, da kuma ba da damar bunkasa noman tumatur a kasar.

Bello Abubakar, shi ne mataimakin daraktan cibiyar binciken fasaha ta Najeriya, ya ce sabuwar fasahar za ta taimakawa kasaar wajen rage adadin kudaden da take kashewa wajen shigo da tumaturin da aka sarrafa daga kasashen ketare.

Abubakar ya ce, a duk shekara Najeriya tana kashe sama da dalar Amurka biliyan 47 wajen shigo da tumaturi daga kasashen waje.

Babban bankin kasar CBN ya ce, Najeriya ce kasar dake kan gaba a nahiyar Afrika wajen samar da tumatur, kuma ita ce kasa ta 13 a duniya, amma kasar tana shigo da tumatur kimanin ton miliyan 66 a duk shekara daga kasashen waje.

A shekarar da ta gabata, wasu masana a kasar, sun yi ta kiraye kirayen a haramta shigo da tumaturin da aka sarrafa daga kasashen waje, suna masu cewa kamfanonin kasar suna da ikon sarrafa tumaturin da ake bukatar amfani da shi a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China