170112-Kwallon-kafar-kasar-Sin-na-janyo-hankalin-duniya-sai-dai-akwai-bukatar-juriya-kafin-kaiwa-ga-cimma-nasara-zainab.m4a
|
A karshen watan Disambar da ya shude, rahotanni sun rika yaduwa game da yadda harkar kwallon kafar Sin ta mamaye labaran kwallon kafar firimiyar Ingila, maimakon batun kulaflikan dake buga wasa a gasar ta Firimiya.
Ga misali a baya bayan nan, kafafen watsa labarai sun yayata shirin da dan kwallon Chelsea Oscar ke yi, na komawa kungiyar Shanghai SIPG, inda aka ce kungiyar za ta saye shi kan kudi har Fan din Ingila miliyan 60, hakan kuwa na zuwa ne kasa da shekara guda, bayan da Chelsea ta sayarwa kasar ta Sin Ramires.
Da yake tsokaci game da hakan, kocin kungiyar Chelsea Antonio Conte, ya ce kasar Sin kalubale ce ga daukacin kulaflikan duniya, bawai kawai kungiyar sa ba. Kalaman dai na Conte na iya zama manuniya, ga irin bunkasar da kasuwar kwallon kafa ta yi a kasar Sin a shekarar 2016 da ta gabata. A wannan shekara kungiyoyin kwallon kafar Sin sun sayi 'yan wasa masu tarin yawa, kan kudade sama da na sauran kulaflika, ciki hadda masu buga gasar Firimiyar Ingila.
Amma abun tambaya a nan shi ne, ko kasar Sin za ta iya yin tasiri a harkar kwallon kafa kamar yadda ta yi a fagen gasar Olympic?. Amsa a nan ita ce, cimma wannan nasara tafiya ce mai nisa ga kasar Sin, amma ko shakka babu kasar ta kuduri aniyar cimma wannan buri.
Kididdiga ta tabbatar da cewa, kungiyoyin kwallon kafar kasar Sin dake buga gasar ajin kwararru ta CSL, sun kashe kudade domin sayen 'yan wasa da yawan su ya kai Euro miliyan 317, wanda hakan ya sanya su zama na farko a duniya, wajen kashe kudade don sayen 'yan wasa a shekarar ta 2016.
Wani shafin yanar gizo mai bayyana musayar 'yan wasa mai suna Trabsfermarket, ya bayyana cewa, ko da aji na biyu na kulaflikan dake buga gasar kwararru a kasar Sin, ya kashe kudaden da suka haura na takwarorin sa dake buga Bundesliga ta kasar Jamus, da La Liga na Sifaniya da kuma kasar Ligue 1 ta Faransa.
Cikin manyan 'yan wasa da suka shigo kwallon kafa a nan kasar Sin cikin shekarar da ta gabata, akwai dan wasan tsakiya na kasar Argentina Ezequiel Lavezzi, da Gervinho na Brazil, da tsohon dan wasan Atletico Madrid Jackson Martinez, da kyaftin din kasar Kamaru Stephane Mbia.
Kaza lika a shekarar ta 2016, sau hudu ana bayyana karya matsayin bajimta wajen sayen 'yan wasa mafiya tsada a kasar ta Sin. Da farko dai kungiyar Jiangsu Suning ta sayi Alex Texeira kan kudi har Euro miliyan 50 daga Shakhtar Donetsk na Ukrainian, duk da irin sha'awar da kungiyar Liverpool ta nuna na sayen dan wasan.
Sai kuma dan wasan kasar Brazil Hulk, wanda a watan Yuni ya koma Shanghai SIPG bisa kwantiragin shekaru 4. An ce kungiyar ta Shanghai SIPG ta sayi dan wasan ne kan kudi har Euro miliyan 55, daga kungiyar Zenit Saint Peterburg ta kasar Rasha. Kaza lika kungiyar ta sayi kaso 70 bisa dari na kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya.
Yanzu kuma batun da ake yi shi ne na sayen san wasan Chelsea wato Oscar dos Santos Emboaba Júnior, wanda a ranar 23 ga watan Disambar da ya gabata Shanghai SIPG ta saye shi kan kudi har Euro miliyan 60.
Da yake tsokaci game da wannan lamari, tsohon kocin kungiyar kwallon kafar kasar Ingila Sven Goran Eriksson, ya ce irin makudan kudi da kulaflikan kasar Sin ke zubawa wajen raya harkar kwallon kafa ne, ke janyo ra'ayin manyan 'yan wasa daga sassan nahiyar Turai zuwa kasar.
Ya ce ya zauna a kasar Italiya a shekarun 1990, a wancan lokaci ko wane dan wasa na burin zuwa Italiya murza leda, saboda kwallo na tashe a kasar. ya ce daga nan sai Ingila wadda a shekarun 2000 ta zamo duniyar 'yan kwallo, a lokacin dukkanin 'yan kwallo na tururuwar zuwa Ingila, saboda manyan kungiyoyi, da kudade da ake kashewa a kasar kan tamaula.
Mr. Eriksson wanda yanzu ke horas da kungiyar Shenzhen FC, ya ce a yanzu kuwa kowa na rububin zuwa Sin, dalilin kudade da ake kashewa wannan harka, wanda kuma ke karawa kungiyoyin kasar karfi matuka.
A baya dai Eriksson ya horas da kungiyar Shanghai SIPG, kafin daga bisani kungiyar ta maye gurbin sa da tsohon kocin chelsea Andre Villas- Boas.
Sauran masu horas da 'yan wasa daga turai, wadanda kasar Sin ta janyo, sun hada da Luiz Felipe Scolari dake horas da Guangzhou Evergrande, da Manuel Pelligrini na Hebei China Fortune, da kuma kocin Shandong Luneng Felix Magath.
Duk dai wadannan abubuwa na nuna yadda harkar kwallon kafar kasar Sin ke dada kusantar takwarorin ta na sauran kasashen duniya.
Matakin shigar da manyan 'yan wasa da bunkasar da gasar ajin kwararru ta kwallon kafar kasar Sin ke dada yi, ta sa harkar ta tamaula kara jan hankalin 'yan kallo.
Game da hakan, shugaban kamfanin CSL Ma Chengquan, ya ce yawan masu bayyana sha'awar su ga kwallon kafa na karuwa cikin sauri, inda ya zuwa karshen shekarar 2016 Sinawa masu sha'awar wasan sun karu da kusan mutum miliyan 5.8. Yayin da kuma yawan masu shiga filayen wasa domin kallo suka kai mutum dubu 24.2, adadin da ya haura na shekarar 2015 da kusan mutum dubi 2.220.
A watan Maris na shekarar da ta shude ne tsohon dan wasan tsakiya na kasar Czech Pavel Nedved, ya maye gurbin tsohon dan kwallon Ingila David Beckham, a matsayin jakadan kwallon kafar kasar Sin ajin kwararru. Da yake tsokaci game da yanayin kwallon kafa a Sin, Nedved ya ce harkar na samun ci gaba, kuma kungiyoyin dake buga gasar ajin kwararru a kasar ko CSL sun kammala wasannin su na kakar 2016 cikin nasara.
Hakan na iya bayyana a fili, idan aka lura da cewa kungiyar kwallon mata ta kasar ta shiga gasar Olympic da ta gabata, bayan wadda aka gudanar a shekarar 2008. A daya bangaren kuma, kungiyar kasar ta maza ta kai ga zagayen karshe na kungiyoyin zakarun nahiyar Asiya, inda ta kusa shiga jerin kungiyoyin da za su buga gasar cin kofin duniya bayan shekaru 15.
Rashin samun wannan dama dai ta sanya kocin kasar Gao Hongbo yin murabus daga aikin horas da kungiyar. Kana aka maye gurbin sa da tsohon kocin Italiya Marcello Lippi a ranar 22 ga watan Oktobar bara.
Ana dai yabawa rawar da Lippi ya taka wajen bunkasa sha'anin kwallon kafar kasar Sin, ko da yake shi ma, ya gaza tallafawa kungiyar kasar kaiwa ga babban burin ta.
Game da hakan, dan wasan baya na kasar Sin da ya taba taka leda a kungiyar Manchester United Sun Jihai, ya ce kwallo a Sin na bukatar 'yan wasa na gida su fara inganta basirar su a gida, su kuma fita kasashen waje domin kara samun horo. Ya ce sai an yi amfani da matasa masu dogon tunani na samun nasara a nan gaba, za a kai ga cimma burin da aka sanya a gaba.
Kungiyar kwallon kafar kasar Sin ta sha gwagwarmaya a fagen tamaula, kuma rabon su da samun gurbi a gasar cin kofin duniya tun shekarar 2002 lokacin da suka halarci gasar, ba tare da zura ko da kwallo daya ba.
Masharhanta na ganin gazawar kasar, na kafa wani ginshiki mai nagarta, shi ne ya haifar da matsalar da ake fuskanta a yanzu haka. Ko da a baya bayan nan, wata kungiyar dalibai ta kwallon kafar kasar Sin ta sha kashi a hannun abokiyar karawar ta ta kasar Japan da ci 9 da 1, wanda hakan ke nuna irin gibi da kasashen biyu ke da shi, a fannin samun horo a fannin tamaula.
Tsohon kocin kungiyar matasa ta kasar Sin Eckhard Krautzun ya bayyana nasa ra'ayi game da hakan, yana mai cewa dole sai Sin ta gina wani ginshiki mai karfi tun daga tushe, wato daga kananan makarantu, yace duk da an dan makara, amma hakan mai yiwuwa ne.
Krautzun na ganin cewa, Sin na da jami'ai da za su iya gina wannan harka ta kwallo daga matakin 'yan wasa matasa, ta yadda nan gaba za su iya gogayya da sauran takwarorin su na sassan duniya. Kaza lika kocin ya ce a yanzu an fi maida hankali ga dauko manyan kociya, domin horas da 'yan wasa a manyan kungiyoyin kasar, amma abu mafi muhimmanci shi ne, komawa mataki na kasa domin horas da matasa da a gaba za su zamo taurari a fagen tamaula.(Saminu Alhassan)