in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guardiola: Akwai banbanci tsakanin Messi da Ronaldo
2016-12-28 19:09:09 cri
Shugaban kungiyar wasan kwallon kafan Manchester City, Pep Guardiola, ya nanata cewa, babu bukatar kwatance a tsakanin yan wasa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, kasancewa koda a tsakanin kasashen Argentine da Portugal ma akwai banbanci.

Ronaldo wanda ya karbi lambar yabo ta Ballon d'Or karo na 4, bayan irin hazakar da ya nuna a wannan shekara. Keftin din kungiyar wasan kasar Portugal ya kuma ciyowa kulub dinsa na Real Madrid lambar yabo a wasannin kwararru na Champions League, kuma shine ya samu lambar yabo a karon farko na wasannin zakarun nahiyar turai a 2016 a wasan Euro France. Sakamakon hakan yasa Guardiola ya sake yin tunanin cewa abune mawuyaci a kwatanta dan wasan da Messi.

Tsohon kociyan na Barcalona ya shedawa taron manema labarai cewa "Messi yafi cancanta, tabbas yafi cancanta, ya san yadda ake buga wasa, ya iya zura kwallo, kuma yana baiwa yan wasan damar taka leda a lokacin wasa."

Ya kara da cewa "tare da girmamawa ga dukkan yan wasa, da farko ga Cristiano Ronaldo, ina taya shi murna, saboda lambar yabo da ya samu. Ina tunanin Messi yana matsayi na gaba."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China