Ya ce "domin cimma buri na na kasancewa a nan, dole na yi hakuri da juriya". Ya ce watana 3 na yi kacal da zuwa nan kuma ina fatan samun damar buga wasanni masu yawa.
Barbosa ya ce salon wasa a Italiya ya banbanta da na gida Brazil, amma duk da haka yana fatan komawa kungiyar ta Milan a watan Janairu bayan hutu, domin ci gaba da buga wasanni kakar bana. Ya ce a tunanin sa idan har zai iya buga wasa a Milan yadda ya kamata, ko shakka babu zai iya buga wasa a ko ina a duniya.
Kalaman na Barbosa dai sun ci karo da na manajan sa Wagner Ribeiro, wanda a farkon watan nan aka jiyo shi na cewa, Barbosa na cikin wani hali, kasancewar ba ya samun damar buga wasanni yadda ya kamata, tun zuwan sa Inter Milan cikin watan Satumbar da ya gabata. Ya ce cikin kusan watanni 4 da ya shafe a kungiyar, wasanni 3 kacal aka bashi damar bugawa.
A baya ma dai wasu kafofin watsa labarai na Brazil sun rika hasashen cewa, mai yiwuwa ne dan wasan mai shekaru 20 a duniya ya koma tsohon kulaf din sa wato Santos, ko Atletico Mineiro, a lokacin musayar 'yan wasa na watan Janairu mai zuwa.(Saminu Alhassan)