Dan wasan mai sheakru 19 a duniya, wanda ya kulla kwantiragi da kungiyar wasan kwallon kafan ta Santos na kasar Brazil wanda zata kare a watan Yunin shekarar 2019, rahotanni sunce masu zawarcin dan wasan sun hada da Monaco, Schalke da Zenit Saint-Petersburg, da kuma Sambafoot.
Maia yace zai yanke hawara game da makomar rayuwarsa ne a ranar 11 ga watan Janairu bayan ya dawo daga hutu.
"Santos da wakilaina zasu yanke shawara idan har lokacin hakan yayi", inji dan wasan tsakiyar.
Maia ya bayyana a kungiyar wasan a karon farko ne sau 91, tun bayan da ya fara aiki da Santos a shekarar 2014. Ya kuma wakilci kasar a wasannin yan kasa da shekaru 17, dana yan kasa da shekaru 20 da kuma matakina 23 l, kuma yana daga cikin rukunin yan wasan da suka yi nasarar lashe gasar zinare a wasannin Rio Olympics a watan Augusta.(Ahmad Fagam)