161229-Jirgin-Chapecoense-ya-tashi-ba-isasshen-mai-zainab.m4a
|
Fasinjojin jirgin su 71 ne suka rasu bayan da jirgin ya tunkuyi wani tudu, jim kadan kafin saukar sa a Medellín na kasar Colombia, a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Har wa yau sakamakon binciken ya bayyana cewa, shi kan sa matukin jirgin Miguel Quiroga, wanda ya rasu yayin hadarin, bai bayyana fuskantar matsalar jirgin ba, sai da lokaci ya yi matukar kurewa.
Sakataren hukumar kula da sufurin jiragen sama na kasar Colombia Freddy Bonilla, ya ce an shake jirgin da kaya, amma babban dalilin faduwar ta sa shi ne rashin sanar da aukuwar matsalar lantarki da jirgin ya fuskanta a kan lokaci, baya ga karanci mai dake cikin jirgin. Ya ce matukin jirgin Quiroga yana sane cewa babu isasshen mai lokacin da zai tashi.
Jami'an hukumar dai sun zargi masu kula da zirga zirgar jirage na kasar Bolivia, da sakaci wajen kyale jirgin ya tashi daga Santa Cruz de la Sierra ba tare da tsarin hanya mai dacewa ba.
Wadanda suka rasu dai sun hada da daukacin 'yan wasan kungiyar ta Chapecoense su 19, tare da daukacin tawagar masu horaswar kungiyar. mutum 6 ne dai kacal suka tsira daga wannan hadari. (Saminu Alhassan)