in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: NUPENG ta shirya shiga yajin aiki na kwanaki 3
2017-01-10 10:02:24 cri
Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya NUPENG, ta ce ta shirya shiga yajin aiki na kwanaki uku tun daga ranar Laraba, domin nuna rashin jin dadinta da kin maida hankali da gwamnatin kasar ta yi game da wasu matsalolin kwadago da suka shafi kungiyar.

Rahotanni dai na cewa tun da fari kungiyar NUPENG din ta bukaci wasu manyan kamfanonin hakar mai dake aiki a kasar, da su maida wasu 'ya'yan tasu 3000 bakin aikin su, bayan da kamfanonin suka sallame su.

NUPENG ta kuma mikawa gwamnatin Najeriyar wasika ta musamman a ranar 16 ga watan Disambar da ya gabata, tana mai neman gwamnatin ta sa baki domin warware takaddamar sassan biyu. Sai dai kuma daga bisani NUPENG din ta yi zargin cewa gwamnatin na yin wasarairai da wannan batu, wanda hakan ne ya sanya ta daukar matakin shiga yajin aiki.

Da yake karin haske game da hakan cikin wata sanarwa da aka fitar, shugaban kungiyar ta NUPENG Igwe Achese, ya ce yajin aikin na kwanaki 3 tamkar jan kunne ne ga dukkanin masu ruwa da tsaki a wannan dambarwa, domin kuma idan ba a dauki matakai da suka wajaba ba, nan gaba za su shiga wani yajin aikin na sai baba ta gani. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China